Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Zarafin Musulmai A Kasar China Ya Ja Hankalin Duniya


Majalisar dokokin Amurka ta yi Allah wadai da mummunan saba hakkokin jama’a da ake yi a yankin Xinjiang a kasar China.

Wani dan Majalisar dokokin Amurka, ya bukaci shugaba Donald Trump, ya tado batun garkame tsirarun mabiya Addinin Islama da yawa da China ke yi, idan ya hadu da shugaban China Xi Jinping, cikin wannan satin.

Dan majalisar Republican Christopher Smith, da ya jagoranci ganawar kwamitin ‘yan majalisar zartarwa da dan jam’iyyar Republican Sanata Marco Rubio, akan batun China.

Dukan su sun gabatar da kudurorinsu a majalisunsu, na yin Allah wadai da mummunar saba hakkokin jama’a da ake yi a akan ‘yan kabilar Uighers dake yamma da yankin Xinjiang.

China ta fuskanci suka daga kasashen duniya, akan yadda ake kulle ‘yan kabilar Uighers, da Kazakhs da kuma wasu tsirarun kabilu. Abinda China ke ikirarin cewa yana da muhimmanci wajen kawar da tsattsauran ra’ayin addini.

Wasu da aka taba tsarewa sun bayyana cibiyoyin a matsayin wuraren da ake canzawa mutane ra’ayi, inda ake tilastawa Musulmai yin watsi da addininsu, ko ace suyi Ridda, su kuma yi mubaya’a da jami’iyyar kwamunisanci dake mulki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG