A yau Asabar ne aka rantsar da Andres Maniel Lopez Obarador, a matsayin shugaban kasar Mexico, wanda ya shiga Ofishin yana da karfin iko, kasancewar jam’iyyar shi keda rinjaye a duka majalinsun dokokin kasar biyu.
Shugaban Lopez yayi ma jama’ar kasar alkawarin zai inganta rayuwar ‘yan kasar, fiye da abun da tsohon shugaban Enrique Pena Nieto mai barin gado yayi, daga cikin abubuwan da ya fada, yace zai sayar da jirgin fadar shugaban kasar.
Lopez mai shekaru 65 wanda baki daya rayuwasa ta ta’allaka ne akan siyasar Mexico. Ya taba zama mamba na jami’iyyar PRI, wanda ta mulki kasar na kimani shekaru 80.
A shekarun 1980 Lopez na daya daga cikin mutanen farko da su ka bar jam’iyyar bayan darewar ta, inda ya koma jam’iyyar PRD.
A shekrar 2000 aka zabi Lopez a matsayin shugaban karamar hukumar Maxico City, birnin tarayyar kasar da yafi yawan jama’a.
A wannan mukamin ya samu karbuwa a idon jama’a, bayan ya kaddamar da wani shiri dake taimakama tsofaffi da marasa hali, kana ya kayatar da babban birnin.
Facebook Forum