Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nigeriya Zata Sami Dala Biliyan Daya Daga Maganin Gargajiya


Magungunan gargajiya
Magungunan gargajiya

Kwararru sun bayyana cewa gwamnatin tarayya zata iya samun kimanin dala biliyan kowacce shekara daga maganin gargajiya sakamon ci gaban da ake kara samu a wannan fannin da kuma kokarin da ake yi na daidaita amfani da magungunan gargajiya da kuma na zamani a asibitai

Kwararru sun bayyana cewa gwamnatin tarayya zata iya samun kimanin dala biliyan kowacce shekara daga maganin gargajiya sakamon ci gaban da ake kara samu a wannan fannin da kuma kokarin da ake yi na daidaita amfani da magungunan gargajiya da kuma na zamani a asibitai. Ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu ne ya bayyana haka a wajen wani bukin baje kolin magungunan gargajiya da aka yi a Abuja.

Shi ma a nashi jawabin, bakon mai jawabin a taron da aka ba lakabi HerbFest 2013, tsohon shugaban hukumar zabe na Najeriya wanda yayi Magana a kan Magana “Abinci a matsayin magani” ya bayyana cewa Najeriya zata iya samun sami kimanin dala biliyan daya kowacce shekara idan ta iya gina sashin maganin gargajiya da sauran su.

Bakon mai jawabin wanda farfesa ne a fannin harhada magunguna, kuma shugaban kungiyar kula da amfani da albarkatun tsira, yace bayan kudin shiga da za’a samu a wannan sashi, zai taimaka wajen rage talauci da rashin aikin yi a kasar. Ya kara da cewa, wadansu kasashen Africa kamarsu Africa ta kudu, Kenya da Ghana da suka gina fannin maganin gargajiyarsu, lafiyayyen abinci da kuma sauran su, suna samun kimanin dala miliyan 3 kowacce rana daga wannan sashin. Haka nan kuma ya kara cewa wannan magungunan suna taimakon ‘yan kasar a fannin kiwon lafiyarsu.

Bisa cewarshi, babu dalilin da zai hana Najeriya samun dala biliyan 1 a kowacce shekara ba daga maganin gargajiya banda ayyukan yi da za a samu da kuma lafiya da al’ummar kasar zasu samu. Yace Najeriya bata cin gaba yadda ya kamata a wannan fannin domin ba a kula a bincike abinda ke faruwa a wadansu bangarorin kasar da kuma ci gaban da ake samu.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG