Yace rashin wadannan, sune suka sa 'yan kasuwa suka zamo 'yan amshin shatar gwamnati, suka zamo sun dogara kusan kacokam a kan gwamnati domin su samu biyan bukatunsu.
A cikin hirar da yayi da VOA, attajirin yace gwamnati ce ya kamata a ce ta dogara kan 'yan kasuwa, domin duk kasar da babu kasuwanci mai karfi cikinta, to ba kasa ba ce. Yayi misali da kasar Kamaru, inda yace ya tafi har ofishin gwamna a Ngaoundere, amma abin mamaki babu wani dan kasuwa kwaya daya tak dake wurin yana jiran ya nemi kwangila.
Ga cikakken bayanin da Alhaji Indimi yayi cikin wannan hira.