Rahotannin kafafen labarai sun ruwaito wasu majiyoyin da aka sakaya su na cewa ana sa ran ganawar ta faru a watan gobe lokacin da Trump ya kai ziyara Turai. Shugabannin biyu na iya ganawa gabanin taron da za’a yi a Brussels daga 11 zuwa 12 ga watan Yuni, ko kuma bayan ziyarar Trump zuwa Burtaniya kwanaki biyu bayan nan.
Mai magana da yawun Majalisar Tsaron kasa Garrett Marquis ya aika da sako ta kafar twitter ranar Alhamis mai cewa, "Ranar 25 zuwa 27 ga watan Yuni, Mai bayar da Shawara Kan Harkokin Tsaron John Bolton zai gana da kawayen Amurka a London da Rome don su tattauna kan kalubalen tsaro, daga nan kuma ya wuce birnin Mascow na kasar Rasha don tattaunawa kan shirin ganawa tsakanin Shugaba Trump da Putin."
Facebook Forum