Wasu ‘yan majalisar wakilai da jam’iyyar PDP sun bayyana cewa babu wani abin bikin ranar dimokaradiyya ta bana, na shekaru 6 na gwamnatin APC.
Shugabannin marasa rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya, sun bayyana cewa gwamnatin jam’iyyar APC ta kasa biyan bukatun ‘yan kasa a shekaru 6 da ta yi tana mulkin kasar.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, jagororin na marasa rinjaye a majalisar ta wakilai, sun bayyana bangaren yaki da matsalar tsaro, da cewa yana daya daga cikin manyan bangarorin da gwamnatin ta shugaba Buhari ta kasa tabuka abin a zo a gani.
Sun ce kasawar gwamnati na magance matsalar tsaro a duk fadin kasar, ya shafi bangarori da dama da suka hada da na aikin gona da tattalin arziki baki daya.
Karin bayani akan: Femi Adeshina, APC, PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Haka kuma sun soki gwamnatin da rashin ingantattun tsare-tsare da manufofi da za su ciyar da kasar a gaba.
To sai dai a nata bangare, fadar ta shugaban kasa cewa tayi shugaba Buhari ya tabuka abin a zo a gani a cikin wadannan shekarun wanda a cikin shekaru 2 masu zuwa wa’adin mulkinsa zai kare.
Fadar gwamnatin Najeriyar dai ta ce sai bayan karkare wa’adin mulkin shugaba Buhari ne jama’ar kasar za su fahimci alheran da ya shuka musu kuma a lokacin ne zasu fara yi masa tarin yabo da jinjina da fatan alheri inda ba za a bar masu adawa da gwamnatinsa a baya ba a wannan lokaci mai zuwa.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar a kan ayyuka da nasarorin da Gwamnatin Buhari ta samu tsawon shekaru shida da ta ke kan karagar mulkin kasar.
Femi Adeshina ya yiwa sanarwar da ya fitar taken ‘Gwamnatin Buhari bayan shekara shida, kidayan Alheranta daya bayan daya’ inda ta ce nan gaba kadan, al’umman kasar za su rika yabawa ayyukansa inda ba za’a bar ’yan adawa a baya ba a lokacin da zai kammala wa’adin mulkinsa.
Kazalika, Femi Adeshina Adesina ya ce, gwamnatin Buhari ta samu nasarori mara misaltuwa a fannonin tattalin arziki wanda hatta masu adawa za su yaba ba tare da son kai ko akidar siyasa ta rufe musu idanu ba tare da yabo.
A yau 29 ga watan Mayun shekarar 2021 ne gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke cika shekara shida, inda Adeshina ke cewa, nasarorin da ta samu za su bude kofar yin nazari a kan tasirin hakan wajen inganta rayuwar al’umman Najeriya da kuma bunkasar kasar.
Adeshina ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu nasarori daga banagren ababen more rayuwa, tattalin ariki, ilimi, kiwon lafiya, wasanni, yaki da cin hanci da rashawa, cigaban al’umma, nasara a alaka da kasashen waje da sauransu, kuma nasarori kadai sun isa zama abun alfahari ga ’yan Najeriya.
Saidai tun bayan wallafa wannan nasarorin da Adeshina ya bayyana cewa shugaba Buhari ya samu ne ‘yan kasar suna fara tlfa albarkacin bakin su kan hasashen inda wasu ke cewa, babu abin alkahiar da su ji ko su ka gani gwamnatin shugaba Buhari ta tabuka.
Daga karshe dai, Femi Adeshina ya ce gaskiya a kullum a bayyane take, sai bayan mulkin gwamnatin shugaba Buhari zasu fara yabawa namijin kokarin da ya yi.