Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Manyan Jami'an Soji 25 Su Yi Ritaya Saboda Nadin Manjo-Janar Yahaya


Babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor (dama) Manjo Janar Farouk Yahaya(hagu) (Twitter/ @HQNigerianArmy)
Babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor (dama) Manjo Janar Farouk Yahaya(hagu) (Twitter/ @HQNigerianArmy)

Sai dai wasu rahotanni na cewa, mai yiwuwa sabon babban hafsan sojin na Najeriya ya nemi wasu daga cikin manyan sojojin su zauna, domin su taimaka da irin kwarewarsu da za a iya bukata.

Akwai fargabar manyan jami’an sojin Najeriya masu mukamin Janar har kusan 25 za su yi murabus na dole, biyo bayan nadin da aka yi wa Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin babban hafsan soji.

A jiya Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janaral Farouk Yahaya a zaman sabon babban hafsan sojin kasa, mako daya bayan rasuwar babban hafsa Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, tare da wasu jami’ai 10 a hatsarin jirgin sama a Kaduna.

Yadda aka yi sallar jana'izar Janar Attahiru da wasu daga cikin sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama (Twitter/ @Daily_Trust)
Yadda aka yi sallar jana'izar Janar Attahiru da wasu daga cikin sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama (Twitter/ @Daily_Trust)

Sai dai kamar yadda aka al’adanta a hukumomin tsaro na kaki, idan aka nada sabon shugaba a cikinsu, wajibi ne dukan jami’an da ke gabansa da mukami su yi murabus.

Kimanin manyan jami’an soji 25 yanzu haka su ke gaba da Yahaya a mukamin gidan soji, wanda hakan na nufin ala tilas su yi murabus, don ba za su yi aiki a karkashin shugabancin wanda suka girma a mukami ba.

Yahaya na cikin manyan jami’an soji ‘yan kwas na 37, haka kuma shi karami akan jami’ai ‘yan kwas na 35 da na 36, wadanda kuma duk za su tafi a murabus kamar yadda ya ke a al’adar soji.

Majalisa Ta Tabbatar Da Tsofaffin Hafsoshin Soji A Matsayin Jakadu
Majalisa Ta Tabbatar Da Tsofaffin Hafsoshin Soji A Matsayin Jakadu

Ko a manyan hafsoshin sojin ma Yahaya karami ne a cikin su, domin kuwa babban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor ya shiga ne ta kwas na 34, yayin da sauran manyan hafsoshin sojin ruwa da na sama, wato Vice Admiral Awwal Gambo da Air Marshal Oladayo Amao, duk suka fito a karkashin kwas na 35.

Janaral Yahaya wanda mamba ne na kwas na 37 na makarantar horas da
Hafsoshin Najeriya (NDA) ya fara samun horo na CADET a ran 27
bakwai ga watan Satumba 1985, bayan ya kare ya fara aiki a sojojin
dake bangaren sojojin Infantry, wato masu yaki gaba da gaba ranar 22
ga watan Satumbar 1990.

Sai dai wasu rahotanni na cewa, akwai yiwuwar sabon babban hafsan sojin na Najeriya ya nemi wasu daga cikin manyan sojojin su zauna, domin su taimaka da irin kwarewarsu da za a iya bukata.

Karin bayani akan: Janaral Farouk Yahaya, sojin Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Janaral Farouk ya yi aikace-aikace da dama a gidan soji kadan daga ciki
shi ne kwamandan Garrison na Birged din mayakan dake kula da tsaron
fadar shuganan kasa, ya kuma koyar a kwalejin horas da manya-manyan
hafsoshin sojojin Najeriya wato Armed Forces Command and Staff College.

Ya kuma rike mukaddashin Darakta a ofishin sakataren rundunar sojin
Najeriya da kuma sashen bincike.

Manjo Janar Farouk Yahaya (Twitter/ Defense Headquarters)
Manjo Janar Farouk Yahaya (Twitter/ Defense Headquarters)

Ya kuma rike mukamin shugaban ma'aikata a rundunar hadin gwiwa dake
aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Niger Delta wato Operation Pulo
Shield. Bugu da kari, ya kuma yi babban jami'i a ofishin ministan tsaron
Najeriya sannan ya yi kwamandan Birged na 4 a rundunar Operation Zaman
lafiya ya kuma yi darakta na ma'aikata a hedkwatar sojojin Najeriya.

Daga nan likkafa ta yi gaba, aka nada shi sakataren rundunar sojojin Najeriya sannan an nada shi babban kwamandan runduna ta daya na
sojojin Najeriya, daga inda kuma daga nan aka nadashi babban
kwamandan rundunar yaki da Boko Haram wato “Theartre Commander, Operation Lafiya Dole” wacce yanzu ta zama “Operation Hadin Kai.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG