Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Na Son Kowa Ya Fara Min Yakin Neman Ta-zarce - Buhari


Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya
Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ba zai yi ta-zarce ba, domin ya riga ya yi ranstuwa da Al-Qur’ani mai girma cewa zai sauka idan wa’adinsa ya kare.

Buhari ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da wasu kungiyoyin ‘yan Najeriya da ke zaune a Saudiyya, kamar yadda kakakinsa Malam Garba Shehu ya fada cikin wata sanarwa da Muryar Amurka ta samu kwafi.

A ranar Litinin Buhari ya isa birnin Riyadh don halartar taron koli na saka hannun jari bisa gayyatar Sarki Salman Abdulaziz Al Saud.

“Na rantse da Qur’ani mai tsarki kan cewa, zan yi aiki bisa kundin tsarin mulki kuma zan tafi idan lokacina ya yi. Ba na son wani ya fara maganar yi min kamfe kan tsawaita mulki domin kundin tsarin mulki bai amince ba. Ba zan lamunci hakan ba.” Buhari ya ce cikin sanarwar.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Kazalika shugaban na Najeriya ya kuma nuna goyon bayansa ga irin rawar da fasahar zamani ke takawa a zabukan Najeriya, yana mai cewa, kaddamar da shirin aiki da na’urar tantance katin masu zabe, da yin amfani da rijista ta na’ura abu ne “da Allah ya amsa addu’arsa, domin sau uku ana zaluntarsa kan nasarorin da ya samu a zabukan da suka wuce” a baya.

“Bayan da aka kada ni a karo na uku, sai na ce musu, akwai Allah. Suka yi ta min dariya, amma kuma sai Allah ya amsa addu’ata ya kawo fasahar zamani. A wannan lokaci, babu wanda ya isa ya sace mana kuri’a ko ya saye su.” Buhari ya ce.

Buhari ya kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnatinsa adalci inda ya ce idan aka kwatanta matsalolin tsaro da aka fuskanta a arewa maso gabashi da kudu maso kudu a shekarar 2015 da yadda suke a yanzu, za a ga cewa al’amura sun inganta.

A ranar Juma’a shugaba Buhar ya kammala ziyarar aiki da ya je a Saudiyya bayan da ya yi sallar Juma’a a Babban Masallacin Makka.

XS
SM
MD
LG