Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban China XI Jinping Ya Rubutawa Buhari Wasika


Shugaba Buhari, hagu da Xi Jinping a dama yayin wata ziyara da ya kai Beijing a 2016
Shugaba Buhari, hagu da Xi Jinping a dama yayin wata ziyara da ya kai Beijing a 2016

Akalla shekaru 50 China da Najeriya suka kwashe suna hulda ta diflomaisyya a tsakaninsu.

Shugaban China Xi Jinping ya rubutowa takwaran aikinsa na Najeriya Muhammadu Buhari wasika inda ya ce China na da burin ganin kawancen da ke tsakanin kasashen biyu ya kai wani babban matsayi.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar dauke da sa hannun kakakin Buhari Femi Adesina ta ce, shugaba Xi ya kwatanta Najeriya a matsayin muhimmiyar kasa a huldar da China ke yi da nahiyar Afirka.

“Dangantakar da ke tsakanin China da Najeriya, ita ce ginshikin kawancen China da nahiyar Afirka.” Shugaba Xi ya fada a cikin wasikar da ya aikawa Buhari yayin da kulla huldar diflomasiyya da kasashen suka yi ta cika shekara 50.

Xi ya aikawa da Buhari wasikar ce a matsayin amsar wasikar da shugaban Najeriya ya aika masa ta taya China murnar cika shekara 72 da kafa Jamhuriyar China.

Shugaban na China ya kara da cewa yana ba yunkurin karfafa dangantakar kasar da China muhimmanci yana mai ba shugaba Buhari tabbacin cewa “China ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen inganta huldar kasashen biyu.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG