Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi wa Najeriya Addu'a Kan Matsalolinta Yayin Aikin Umara


Shugaba Buhari da tawagarsa (Facebook/Fadar shugaban kasa)
Shugaba Buhari da tawagarsa (Facebook/Fadar shugaban kasa)

A ranar Litinin Buhari ya isa birnin Riyadh don halartar taron koli na saka hannun jari bisa gayyatar Sarki Salman Abdulaziz Al Saud.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gudanar da aikin Umara yayin ziyarar aiki da yake yi a kasar Saudiyya.

Wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce da safiyar ranar Alhamis shugaba Buhari ya gudanar da aikin na Umara.

“A lokacin da Buhari ya isa Babban Masallacin Makka, wasu jami’ai da dakarun tsron masallacin sun tarbe shi.” Sanarwar ta Malam Garba ta ce.

“Kamar yadda koyarwar addinin Islama ta tanada, an yi addu’o’i ga Najeriya kan kalubalen da take fuskanta, musamman matsalolin tsaro, rashin hadin kai da kuma samun kyakkyawar makoma ga al’umar kasar.”

A dai ranar Litinin Buhari ya isa birnin Riyadh don halartar taron koli na saka hannun jari bisa gayyatar Sarki Salman Abdulaziz Al Saud.

A cikin tawagar Buhari, akwai Ministan kasuwanci da masana’antu da saka hannun jari da ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta yanar gizo da kuma kananan ministoci na harkokin waje da man fetur.

XS
SM
MD
LG