A hirar shi da Muryar Amurka, Malam Garba Shehu, babban jami’in yada labarai a fadar gwamnatin, kuma daya daga cikin tawagar Shugaban ‘kasar ya bayyana cewa, taron wanda ya ke hada kan shugabanni na kasashen duniya da masu zuba jari, dama ce ga Najeriya ta tallata kanta da kuma kulla huldar kasuwanci da masu zuba jari.
Garba Shehu yace bisa ga taken taron na bana, "Zuba jari don bunkasa rayuwar al'umma" taron yana da muhimmanci domin burin gwamnati ke nan ganin an inganta rayuwar al'umma. Yace a duniya duka kowa ya san cewa, ana zuba jari domin a fadada kamfani, don a ci riba. abinda kuma a ke so a yi a wannan taron shi ne a jawo hankalin masu zuba jari, su zuba jari don a taimaki al'ummomi wadanda ya ke an bar su a baya kamar Najeriya.
Yace duk fitunun da ake fuskanta a duniya, yake-yake, da ta'addanci babu abin da ya ke haddasa shi face talauci. saboda haka idan za a sami kamfanoni da masu zuba jari su zo su kafa kamfanoni, su bunkasa tattalin arziki, don a taimakawa al'umma su fita daga cikin rashi, marar shi ya samu to wannan shi ne zai kawo zaman lafiya a duniy baki daya.
Kakakin shugaban kasar ya ce kwanan nan shugaba Buhari ya sa hannu a dokar da za ta canza lamuran yadda ake gudanar da harkokin man fetir da suka hada da yadda ake haka da sayarwa da cikinin man fetir a Najeriya wanda aka yi domin ya fadada wanda duk ya ke so ya zo ya zuba jari a kasar.
Ya bayyana cewa a wannan taron, shugaba Muhammadu Buhari zai tallata irin canje canjen da ake samu wajen fadada tono mu'adinai da dokoki da ake yi masu saukaka shigowa jari kuma a fitar da shi ba tare da jinkiri ba.
voahausa.com/a/ziyarar-aiki-da-shugaba-buhari-keyi-a-saudiyya
voahausa.com/a/buhari-ya-tafi-kasar-habasha
buhari-ya-isa-paris-zai-gana-da-macron-kan-matsalar-tsaro
buhari-zai-je-london-taro-daga-nan-zai-duba-lafiyarsa
Saurari cikakken rahoton da Umar Faruk ya hada: