Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Zai Tafi Burtaniya Hutu


Tinubu a cikin jirgin sama
Tinubu a cikin jirgin sama

Bayo Onanuga, yace Tinubu zai yi amfani da makonni 2 ne a matsayin hutun dake hade da aiki domin sake nazarin sauye-sauyen gwamnatinsa akan tattalin arziki

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa Burtaniya a yau Laraba domin fara hutun makonni 2 a wani bangare na hutunsa na shekara.

Sanarwar da mataimakinsa na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a yau tace Tinubu zai yi amfani da makonni 2 ne a matsayin hutun dake hade da aiki domin sake nazarin sauye-sauyen gwamnatinsa akan tattalin arziki.

Zai dawo gida Najeriya bayan karewar hutun nasa.

Shugaba Tinubu ya gudanar da bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya na 64 ta hanyar gabatar da jawabi, inda ya shaida cewar gwamnatin tarayya na shirin bijiro da wani taron kasa na kwanaki 30 da nufin shigar da matasa cikin gwamnatinsa.

Ya kara da cewar nan bada jimawa ba za a fito da tsare-tsaren taron da kuma hanyoyin da za a zabo wakilan da zasu halarce shi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG