Yace tun daga yau asabar, kowa yana iya fita yaje harkarsa har zuwa karfe 9 na dare, lokacin da aka saba komawa gidaje har zuwa karfe 6 na asuba.
Mataimakin gwamnan ya roki jama'ar Maiduguri da na Borno da su bayar da cikakken hadin kai ga sojoji da sauran jami'an tsaro da ma yaran nan da ake kira "yan Gora ko Civilian JTF, ta hanyar tsayawa da bin umurnin jami'an tsaro a duk inda ake gudanar da aikin binciken mutane da ababen hawa.
Alhaji Zanna Umar Mustapha ya bayyana hamdala cewar sojoji da jama'a sun samu nasara a kan 'yan bindigar da suka kai hari, yana mai cewa da safiyar yau asabar ma sojojin sun bi sawu tare da kai farmaki a kan wasu daga cikin tsageran da suka kubuta suka yi kokarin gudu su bar gari.
Yace da ikon Allah an fara ganin karshen wadannan tsagera ke nan.