Alokacin da aka rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar 29 ga wata mayun watan jiya ne ya koka ga yadda halin tattalin arzikin Najeriya ke halin mashashshara, wanda ke bukatar farfado da shi cikin gaggawa.
Sabon shugaban na Najeriya yace fadowar farashin man fetur da matsalolin tsaro yawan rashin aikin yi musamman da ga cikin matasa yana daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantan tattalin arzikin Najeriya.
Abin damuwa anan shine yadda ‘yan Najeriya ke bukatar ganin canji da gaggawa, matasa daga birnin Kano sun bayyanawa wakiliyar Dandali Baraka Bashir yadda suke neman sabuwar gwamnatin da ta kawo musu canji a cikin gaggawa.
A tabakin wani masanin harkar tattalin arzikin kasa yace, bai kamata ba Najeriya ta dogara akan ‘danyan man fetur domin kuwa da akwai hanyoyin samun kudin shiga masu dinbin yawa da gwamnati zata iya amfanin da su wajen samarwa kasa kudin shiga, wanda suka hada da samar da wutar lantarki da makamashi da gina masana’antu domin samarwa da matasa ayyukan yi.