Majalisar Fiqhu ta Duniya mai hedkwata a kasar Sa’udiyya, ta ce wannan babban laifin da ‘yan tsagera irinsu Boko Haram suke aikatawa, ya saba da akidojin imani, ya kuma saba da koyarwar Qur’ani da Sunnah.
Ita ma Hukumar Kare Hakkin Bil Adama mai zaman kanta ta Kungiyar Kasashen Musulmin Duniya, OIC, ta bayyana fusatarta da sace dalibai mata su fiye da 200 na Chibok da aka yi, da kuma ikirarin da kungiyar Boko Haram ta yi cewar ita ce ta aikata wannan ta’asa.
Hukumar ta bayyana tsananin bakin cikinta da bahaguwar hujjar da madugun ‘yan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayar cewa wai sace ‘yan matan da barazanar sayarda su, akidar Musulunci ce.
Hukumar ta ce sace wadannan yara, ya karya dokokin Musulunci a saboda ya tauye musu ‘yancin da Musulunci ya ba su na neman ilmi, da zama cikin lumana, da mutuncinsu.
Dukkan cibiyoyin biyu sun yi Allah wadarai da kungiyar Boko Haram da ayyukan da suka ce tana yi na bakanta addinin Musulunci.