Wani minister a Najeriya yce tarzomar addini da kablianci dake faruwa a wasu sassan tsakiyar kasar ba zai kassara zaben kasar cikin watan Afrilu ba.
Akalla an kashe mutane metan galibi cikin jihar Flato,inda tsagerun kirista da musulmi suka yi ta kai hare hare da daukar fansa da aka fara tun wani harin boma bomai a jajiberen kirsimeti,day a halaka mutane 80.
Lamarin ya kara tabarbarewa da take taken ‘yan kungiyar Boko Haram masu zazzafar ra’ayin Islama, da hukumomi suke aibantawa da hare hare da ake kaiwa kan jami’an tsaro dana gwamnati.
‘Yansanda sun fada jiya Talata cewa ‘yan bindiga da ake zargi daga kungiyar Boko haram ce sun kashe wani babban jami’in ‘yansanda a birnin Maiduguri. A hira day a yi d a MA ministan ‘yansandan Naigeria Humphrey Abbah yace za’a yi zaben watan Afrilu cikin lumana.Yace gwamnati zata iya shawo kan tarozmar,kuma ta fara daukan matakai domin haka.
Birgediya Janar Hassan Umaru yace rundunar sojojin tana sake canja sojoji sojojin dake aiki cikin d aaka tura domin tabbatar da doka da oda. Muna da akrin bayani bayan labaran Duniya.