Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sake gano kaburburan mutane masu yawa a yashe a Ivory Coast


Morsi supporters are seen at a protest at Cairo's Rabaa al-Adawiya Square, the focal point of their sit-in, July 27, 2013.
Morsi supporters are seen at a protest at Cairo's Rabaa al-Adawiya Square, the focal point of their sit-in, July 27, 2013.

Jami’an dake gudanar da bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce sun gano kabarurrukan mutane masu yawa a Ivory Coast dake dauke da gawarwakin mutane sama da hamsin.

Jami’an binciken dake aiki tare da jami’an ofishin kare hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ran litinin, suka bayyana cewar sun gano kabarurrukan mutanen ne a Unguwannin dake wajen birnin Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast. Mazuna unguwannin sun bada shaidarcewa gawarwakin da aka gani na wadanda aka kashe ne a ran 12 ga watan Afrilun da ya gabata lokacin da ‘yan bindiga dake goyon bayan hambararren shugaba Laurent Gbagbo suka kaiwa masu goyon bayan sabon shugaba Ouattara hare-hare domin tsoratasu.

Jami’an hukumar kare hakkin Bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya sun bada sanarwar cewa sun fara gudanar da binciken rahotannin da aka bayar dake cewa an gano wasu kabarurruka a yashe a unguwannin Yopougon, ana kuma kyautata cewar gawarwakin farar hular da aka yiwa kisan gilla da ake zargin sassan biyu dake gaba da juna da aikatawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG