Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Na Cigaba Da Yunkurin Dauki-Dora


Bukola Saraki (2nd L) takes the oath of office as the senate president of the 8th Nigeria Assembly in Abuja, Nigeria June 9, 2015. Also pictured are Senator Dino Melaye (L), Senator Sani Yerima and National Assembly Clerk Salisu Maikasuwa (R). REUTERS/Af
Bukola Saraki (2nd L) takes the oath of office as the senate president of the 8th Nigeria Assembly in Abuja, Nigeria June 9, 2015. Also pictured are Senator Dino Melaye (L), Senator Sani Yerima and National Assembly Clerk Salisu Maikasuwa (R). REUTERS/Af

Jam’iyyar APC mai rinjaye a majalisun dokokin Najeriya tace biyo bayan sulhu musamman ma na ‘yan majalisar dattawa ne ya sanya ta aika jerin sunaye da take so a baiwa sauran manyan mukamai a majalisar.

Binciken da Muryar Amurka ta gudanar ya nuna cewa APC na so a nada Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban masu rinjaye, inda George Akuma zai zama mataimaki.

Shi kuwa Farfesa Shola Adeyeye mai tsawatawa, Habu Ibrahim mataimaki.

Mai Mala Buni, shine sakataren APC “a jam’iyyance mun rubuta wa shi shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai a matsayinsu na ‘ya’yan jam’iyyar APC abunda muke bukata a gare su, shine su bi umarnin jam’iyya. Shine yanzu abunda jam’iyya take jira daga gare su.”

Idan ba’a manta ba, dattawan dake mara baya ga Bukola Saraki na gani da jam’iyyar ta basu damar zaben wadannan mukaman a tsakaninsu maimakon turo sunaye da zai zama kamar fifita wasu kan wasu.

Danjuma Goje dan majalisar dattawa ne “a dai yadda aka saba yi, tun daga farkon wannan demokradiyya duk shuwagabanni na wannan majalisar dattawa, su Sanatoci su ke zama su zabi shuwagabanninsu.”

Shin majalisar zata amince da sakon uwar jam’iyyar, ko dai za’a maimaita tarihin baya ne? ‘Yan majalisar dai saura kadan wadansunsu su kaure da fada, tsakanin masu goyon bayan wasikar jam’iyya, da masu son a bari mai rabo ya dauka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG