Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An tashi baram-baram a taron Sanatocin Najeriya


Sanata Bukola Saraki, sabon shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Bukola Saraki, sabon shugaban Majalisar Dattawa

Badakar shugabancin majalisar dattawan Najeriya na ci gaba da sama da kasa. Wanda har yanzu tsuguno bata kare ba, don uwar jam’iyyar APC na taro ‘ya’yan jam’iyyar ma na nasu, kamar yadda wakiliyarmu Madina Dauda ta shaida mana.

Baya ga zaman majalisa da ‘yan majalisa ke yi, wannan shine karo na biyu da Sanatocin jam’iyyar APC na bangarorin nan na Unity Forum da na Like minds suke taron warware matasalar badakalar zaben majalisa.

Sun taru da niyyar warware matsala, amma sai taron ya tashi baram-baram ba yadda aka so ba. Sanata Kabiru garba Marafa yace ba nasarar Bukola Saraki ce ta dame su ba, amma saba ka’idar da aka y ice matsalar.

Har yanzu dai ba su sami damar zaben shugaban marar sa rinjayen majalisar ba. Sanata Marafa yace kawai wayar gari suka yi suka ga an shigo musu da wani sabon kundin dokoki ba tare da bin tsarin yin gyara gareshi ba idan bukatar hakan ta taso.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG