Sakin wadanda ake tuhuma da akasarinsu matasa na zaman jiran Shara’a, saboda tuhumarsu da aikata kananan laifuffuka na daga cikin wani bangare na kokarin da ma’aikatar Shara’a keyi na rage cunkoso a gidajen Yari.
Mai Shara’a Banu, ya ce rukunin na wadanda aka saka sun hada da wadanda shekarunsu na haihuwa ya gaza goma sha takwas, masu fama larura na rashin koshin lafiya da kuma wadanda suka yi zaman wakafi fiye da wa’adin laifukan da ake tuhumarsu ko da an iske su da laifi gaban Shara’a.
Yusu Ibrahim da Isa Musa na Goggo wasu daga cikin wadanda aka yiwa afuwa sun nuna nadama tare da alkawarin zama mutane na gari a wata hira aka yi da su bayan sakin nasu daga gidan Maza.
Wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu, ya halarci zaman kwamitin ya ce akwai mutane Dari Shida da Tamanin da Biyar a gidan Yarin Jimeta, wanda aka gina don mutane Dari Uku kacal. Daga cikin wannan adadin Dari Uku da Casa’in da Shida na zaman jiran Shara’a ne.
Saurari cikakken rahotan Sanusi Adamu.