Yau ce ranar da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta fadi cewa kasar Najeriya ta rabu da cutar Ebola.
Dr. Halliru Alhassan, ministan kiwon lafiya, ya nuna farin cikin sa akan nasarar da aka samu wajen yakar cutar Ebola da kuma mika godiya ga al’ummar kasar Najeriya da suka bada hadin kai, da jami’an kiwon lafiya, da ‘yan jarida da kuma gwamnatin shugaba Jonathan wajen yakar cutar.
Da yake bayani a wata hira da muryar Amurka, Dr. Halliru yace babbar hanyar da aka bi wajen dakile bazuwar cutar itace samun shugabancin mai kyau daga Goodluck Jonathan, amma yayi gargadin cewa har yanzu akwai barazanar cutar muddin mutum daya na dauke da cutar a duniya, za ta iya bazuwa. Don haka yayi kira da a cigaba da kiyaye duk Matakan hana yaduwar cutar.
Dr. Halliru kuma ya fadi cewa Najeriya ta bada gudunmuwar kudi ga kasashen da ke fama da cutar yanzu haka kuma tana horar da jami’an kiwon lafiya don taimakawa a kasashen.