Ana ta samun rahotannin da suka saba ma juna a kan ainihin musabbabin wannan fada, da yawan mutanen da suka mutu, bda kuma irin barnar da aka yi. Hukumomin Najeriya sun ce mutane talatin da wani abu suka mutu, yayin da jami'an agaji da na Jihar Borno suka ambaci mutane akalla 187. Sanata mai wakiltar Baga, Maina Maaji Lawal, shi kuma yace mutane 228 aka kashe a garin.
A jiya talata kuma, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch, ta fito da wasu hotunan da aka dauka da tauraron dan Adam na garin Baga kafin lokacin fadan da kuma bayansa, inda a ciki ta ce ta lissafa gidaje akalla dubu 2 da dari biyu da saba'in da biyar da aka kona ko aka lalata.
Dr. Aliyu Tilde yace ba yau ne aka saba ganin irin wannan barna da sojoji suke yi idan an taba wani nasu, yana mai yin misali da abinda ya faru a garin Zaki Biam na Jihar Binuwai da wasu wuraren.
Ga cikakken bayanin Dr. Tilde: