Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Yin Zanga Zanga Kan Ziyarar Da Shugaba Trump Zai Kai Landan


Shugaban Amurka Donald Trump zai kai ziyarar aiki Birtaniya ranar 12 ga watan Yuli nan , wannan ita ce ziyarar sa ta farko a matsayin shi na Shugaban kasar Amurka zuwa kasar Biritaniya. Ziyarar da zai kai ta aiki ce, ma’ana ba za ‘a gayyace shi ya hadu da sarauniyar Ingila Elizabeth ba.

Anyi ta jirkinta ziyarar biyo bayan adawar yan siyasa da adawar dubban mutanen Ingila, wadanda suke shirin yin zanga zanga akan tituna domin kin amince wa da ziyarar.

Wata yar kasar Ingila, mazauniyar Landan, mai suna Terry, ta fadawa muryar Amurka cewa “zan fito domin nuna adawata akan ziyarar da ake shirin yi, ni ba mutum bace mai son nuna ra’ayi na a bayanar jama’a ba, amma a gani na bai dace a ce yazo ba.”

Magoya bayan shugaba Trump na fargabar cewa tarukan zanga-zangar na iya toshe tasirin ziyarar tashi a can Biritaniya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG