Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kilomitoci Kadan Ya Ragewa Dakarun Siriya Su Shiga Birnin Al-Bab


Motar Yan Tawayen Siriya Da Turkiya Ke Goyawa Baya.
Motar Yan Tawayen Siriya Da Turkiya Ke Goyawa Baya.

Mayakan 'yan tawaye da ma na gwamnatin kasar Syria sun dirkaki tungar 'yan kungiyar Daesh a garin al-Bab dake arewacin Syria

Mayakan 'yan tawaye Siriya masu samun goyon bayan Turkiyya, sun kutsa inda mayakan ISIS ke da karfi a Al-Bab dake Arewacin Siriya a ranar Asabar, yayinda Sojojin gwamnatin Siriya da Rasha ke goyon baya suka dakata da cigaba da harinsu a inda aka ja daga domin raba Abokanan gabar haduwa.

Wadanda suka shaida al’amarin sun bada rahoton mummunan fada a Al-Bab kilomita 40 Kudancin iyakar Turkiya amma babu rahoton rashin rayuka har izuwa yanzu.

A wani sako daban Ministan harkokin wajen Rasha yace dakarun gwamnatin siriya da Rasha ke goyawa baya “sun yanta wani gari mai suna Tadef wanda ministan ya bayyana a matsayin Wajen da ISIS ke da karfi fiye da ko’ina a kusa da Birnin na Al-Bab.”

Har yazuwa daren Asabar Siriya ko kuma yan Sai’do basu tabbatar da wanan batu ba.

Kasan cewar kilomitoci kadan ya rage wa Dakarun Siriya su shiga Al-Bab da kuma Sojojin Yan tawaye da Turkiya ke goyawa baya na kara kutsa kai cikin birnin, wasu masu fashin baki sunyi gargadin yiwuwar barkewar wani sabon tashin hankalin da bangarorin guda biyu wanda zai baiwa Mayakan ISI damar guduwa daga wurin da yawa ba tare da kwarzaneba.

Masu fashin baki dai sun bayyana Arewacin Siriya a matsayin wajen da yafi ko’ina sarkakiyar filin yaki da bangarorin yakin da dama,tun da yakin ya barke a shekarar 2011 wanda yayi sanadiyar rayuka kusan 400.000.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG