WASHINGTON, DC —
Kakakin majalisar dokokin jamhuriyar Nijar Hamma Ahmadu yace baya hana kansa barci dangane da rade raden cewa za’a tsige shi daga kan mukaminsa.
Hamma wanda yake magana da manema labarai a karo na farko bayan harin da aka kai kan gidansa cikin watan jiya, yace Allah ne yake bada mulki kuma shine yake kwacewa. Bai zaci dama zai zama kakakin majalisa ba, kuma kamin ya karbi wannan mukami mutane nawa ne suka rike shugabancin majalisar dokokin Nijar.
Gameda harin da aka kai gidansa zamanin yana kasashen waje, Hamma yayi Allah wadai da harin yace har abada ba zai yafe ba, yana kuma rokon Allah ya hana maharan samun biyan bukatunsu na duniya da lahira.
Ga karin bayani.