Masu ruwa da tsaki sun yi taro da aka shirya a tsaunin Mambilla da zimmar fadakar da al'umman yankin game da hatsuran dake akwai a wannan aiki na madatsar ruwan Mambilla.
A taron dai an fadakar da al'umman ne na irin fa'idar dake akwai kana kuma da manyan kayakin aiki da za'a zo dasu da hakan yasa aka gargadi jama'a da su kula.
Gwamnan jihar Taraba Architect Darius Isiyaku wanda kwamishinan makamashi Hon Garba ya wakilce shi, ya ce gwamnatin jihar zata ci gaba da bada hadin kai don ganin an samu nasarar aiwatar da aikin.
“Yace mun zo ne mu wayar wa da alumma kai game da inda za’ayi dam din da kuma irin amfanin da za’a samu matsalolin da ka iya faruwa.”
Ya kara da cewa, zasu fadakar da jama’a game da tsoro da aka cusa musu dangane da Dam din da batun filayensu da aka gaya musu wai gwamnati zata kwace musu.
Ministan makamashi Engineer Sale Mamman, Wanda hadiminsa Emmanuel Bello ya wakilce shi a wannan taro da ya hada da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki ya zayyano manufar wannan shiri.
Yace, za’a kai kwararru su gudanar da tantancewa kuma za’a biya mutane kudinsu na filaye da aka karba a hannunsu. Ministan ya kara da cewa, wannan shine farkon aikin da za’a yi, inda ake sa ran sarakuna da sauran shugabannin al’umma zasu fadakar game da muhimmancin wannan aiki.
An shafe fiye da shekaru 30 ana batun wannan aiki na madatsar Mambila.
Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz cikin sauti:
Facebook Forum