Da yake mika tallafin shahararren Dankasuwan yace yazo jihar Taraban ne, domin jifar tsuntsaye uku da dutse daya, na farko ya jajantawa al’umman jihar bisa rayukan da suka salwanta, a yankin Mambillan, kana ya jajantawa gwamnatin jihar bisa rasuwar tsohon gwamnan jihar Danbaba Suntai, kana daga karshe ya kamalla yarjejeniyar dake tsakanin sa da gwamnatin jihar na batun kamfanonin da yake son kafawa na noman shinkafa da rake a yankin Lau.
Yace, ‘’ da farko bari ya soma jajantawa bisa rayukan da muka rasa a Mambilla da kuma na tsohon gwamnan jihar Danbaba Suntai wanda a zamaninsa ne suka soma wannan batu. Allah Ya bada hakurin rashi, kuma a kan haka nema suke son su dan bada tasu tallafin domin taimakawa wadanda rikicin Mambillan ya shafa na kudi naira miliyan 50. Da fatan Allah Ya kare na gaba.
Bayan haka kuma, yace wannan batu na noman rake da shinkafa a shirye suke su fara wannan aikin, kuma zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, da cimaka a kasa, dole su tashi wajen habaka harkar noma,’’ a cewar Dangoten.
Gwamnan jihar Taraban Arch.Darius Dickson Isiyaku wanda shi ya tarbi dan kasuwan ya soma ne da bayyana matakan da gwamnatin jihar ke dauka a yanzu na maido da doka da oda a yankunan da rikicin ya shafa .
‘Yace, kamar abinda ya faru a Manbila gaskiya abu ne da zai bata wa mutum rai ne, ba abu ne da ya kamata yakai ga fada ko kuma kashe-kashe ba, amma tunda ya faru yanzu suna muna rokon mutane suyi hankuri, su hakura da juna kuma sun tura mutane su roke su. Yace sun gode ALLAH dai yanzu kome ya kwanta kuma suna nan suna kokarin ganin zaman lafiyan ya zaman a din-din-din, su kuma wadanda suka yi laifi , ba samu kyale su ba’’
Ga Ibrahim AbdsulAzeez da Karin bayani
Facebook Forum