Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Sojoji Basu da Hurumin Katsalandar a Zabe


Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Air Marshal Alex Badeh.
Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Air Marshal Alex Badeh.

A dai-dai lokacin da aka yi ganawa da shugaban hukumar zabe, Farfesa Attahiru Jega, da ‘yan majalisar dattawan Najeriya, dagane da shirye-shiryen zaben da za’a gudanar a wata mai zuwa, to fa ta bayyana cewa Sojojin Najeriya, da suka bada shawarar a dage zabe basu da hujjar yin haka a bisa ga doka.

Lauya Solomon Dalung, wanda ya furta haka a wata hira da wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, yace “bisa ga dokokinmu na tsarin mulki basu da wani hurumi, a dokoki na aikinsu na Soja basu da hurumi, domin su suna da dangantaka da shugaban kasa ne kawai, kuma duk wani rubutun da zasu yiwa shugaban kasa zasu bashi shawara, shi shugaban kasa ne mai baiwa shi shugaban hukumar zabe shawara, kuma zai yi wannan ne bayan ya karbi shawarwari na tsaro, sai ya kira majalisar tsaro na kasa su tattauna, wanda ya kunshi Gwamnonin na adawa da masu mulkin kasa, sa a duba bayan mahawara shine za’a aikawa hukumar zaben, amma rubutawa shugaban hukumar zabe kai tsaye wato an raba shi da ikon cin gashin kansa da doka ta tanada.”

Mr. Dalung ya kara da cewa “a karkashin demokradiyya na kwarai, kuma idan shugaban zai yiwa kasa adalci, yakamata ya raba wadannan mutanen da aikinsu domin sun wuce gona da iri, kuma matakin da suka dauka nada hadarin gaske wanda idan ba don hakurin da shuwagabanin suka baiwa ‘yan Najeriya ba, da yanzu ba maganar zabe mu keyi ba.”

Idan ba'a manta ba a kwanakin baya ne shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya mai zaman kanta, wato INEC ta bayyana cewa dole da dage babban zaben kasa daga watan Fabrairu zuwa watan Maris, saboda hukumomin tsaro baza su samu damar samar da tsaro ba a lokutan zabe. Wannan mataki ya jawo korafe-korafe da Allah wadai a duk fadin Najeriya.

XS
SM
MD
LG