Alhaji Ibrahim Sulu Gambari wanda ya samu wakilcin Magajin Indan Ilori Alhaji Salihu Woru a taron masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro a Ilori. A jawabinsa ya ce dole ne mu hada hannu mu yaki ta'adancin da ya addabi kasarmu. Ya ce ko dan jarida ne ko dan kasuwa ne ko wanzami ne ko 'yansanda a hada hannu a yaki laifuka. Kana ya kara da cewa su 'yansanda su zama abokanan jama'a. Ya ce babu wani adalci game da aikata laifi. Dole ne al'umma su zama masu gaskiya. Ya ce domin mutum bashi da aikin yi ba hujja ba ce ta aikata laifi.
Jami'in tsaro na 'yansandan ciki na jihar Kwara Mr. Kadiri Olarewaju Ibrahim ya ce jami'ansu suna kowane lunguna da zarar wani abu ya faru zasu damke mutum don hana barkewar tashin hankali.
Taron ya samu halartar jami'an tsaro daga rundunoni da dama.
Hassan Umar Tambuwal nada karin bayani.
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”