Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Sun Koka Da Kara Wa'adin Dokar Ta Baci


Sojojin dokar ta baci a Adamawa
Sojojin dokar ta baci a Adamawa

Kara wa'adin dokar ta baci da gwamnatin Najeriya ta yi a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar ya tada jijiyoyin wuyan mata

Kwana kwanan nan gwamnatin Najeriya ta kara wa'adin dokar ta baci da ta kakabawa jihohin Adamawa, Borno, da Yobe a arewa maso gabashin kasar domin ta'adancin da Boko Haram keyi wanda ya kara tsamari a Borno.

To sai dai kungiyoyin mata a jihar Adamawa sun kira gwamnatin tarayya ta tausaya masu domin, injisu, su ne dokar tafi shafa da matsaloli. Matan sun ce tun lokacin hare-haren mata ne aka fi bari da marayu domin kashe mazajensu da ake yi.

Matan Adamawa sun ce kara wa'adin dokar a jiharsu ba wani abu ba ne illa siyasa. Cikin wata shidan wa'adin farko na dokar babu mutum daya da aka kashe a jihar sabili da aikin ta'adancin na kowace kungiya. Bugu da kari babu wani tashin hankali da aka yi a jihar. Suka ce suna cikin murnar rikici ya kare a jiharsu sai kuma wai an sake kara masu wa'adin dokar. A ganisu wata manakisa ce ake yi masu domin aga an yi tashin hankali. Matan suka ce da Kristoci da Musulmai duk suna zaman lafiya kuma da ikon Allah babu abun da zai faru.

Wata Farfasa Hauwa Abdu Biu ta ce mata na cikin matsala. Wasu su kan shiga yawo da 'ya'yansu suna bara domin neman abun da zasu ci. Ya kamata a san abun da za'a taimakawa mata domin suna matukar bukatar taimako. A yi kokari a tara matan a san irin matsalolin da suke ciki. Mata da suke cikin wadannan jihohin suna fama. Gwamnati ta taimaka. Su ma da suke da hali zasu taimaka idan an kirasu. A saka mata cikin kungiyar da za'a iya koya masu sana'o'i wadanda zasu iya yi domin su rufa ma kansu asiri.

To sai dai a wani gangami da aka yi a gidan gwamnati, gwamnan jihar Murtala Nyako ya godewa jama'ar jihar domin hadin kan da suka bayar tun lokacin da aka kafa dokar ta bacin. Gwamnan ya kuma nuna bacin ransa da wadanda ya kira 'yan siyasan Abuja da suke jawo ma jihar masifa. Ya roki Allah ya saka ma jihar.

Ga Ibrahim Abdulaziz da rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye


LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG