Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kai Komo A Kan Batun Makaman Nukiliyar Korea TA Arewa


Shugaba Trump da shugaba Kim
Shugaba Trump da shugaba Kim

Wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya hakikance cewa Korea ta Arewa yakamata ta fara nunawa Amurka alamar zata cika alkawari, idan Pyongyang din tana bukatar komawa kan teburin tattaunawa da Amurka.

Masu tattaunawa daga Amurka da Korea ta Kudu suna kai komo a kan batun kawo karshen shirin kera makaman nukiliyar Korea ta Arewa da aka cimma a cikin watan Yuni, a taron kolin tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da na Korea ta Arewa Kim Jong Un.

Duk da nasarorin da ake hasashen samu, akwai kuma cikas da ake huskanta na rashin samun tabbas daga Korea ta Arewa da kuma bukatunta ga na neman tabbacin tsaro da kuma yi mata wasu alkaura kafin ta amince ta wargaza makamanta nukiliyarta.

Amma shi babban jami’in na Amurka, Andrea Thompson mai kula da tattalin makamai da tsaron kasa da kasa karkashin sakataren harkokin wajen Amurka, ya fadawa manema labarai a nan Washington jiya Juma’a cewa, ba zasu baiwa Korea ta Arewa wani tabbaci ba, har sai ta aiwatar da abubuwa da ta fada a baya.

Yace yakamata jami’ai daga Pyongyang su fara daukar matakin aiwatar da bangarensu na yarjejeniyar da aka kulla a Singapore, yana nufin alkawarin da suka dauka na wargaza makamansu na nukiliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG