LEGOS, NIGERIA - Matakin da Majalisar ta dauka in ji kakakin Majalisar, Mudassir Obasa, ya biyo bayan kukan da mahaifiyar yaron Madam Abiodun Deborah ta gabatar, inda ta ce an yi wa ‘dan ta mai suna Adebola Akin Bright aiki a asibitin, maimakon ya samu kan cutar da ke damun sa, sai kuma wata sabuwar cuta ta taso, bayan nan ne aka gano akwai aikin ganganci wajen yi wa yaron tiyata, lamarin da kuma ya kai ga lallacewa ko bacewar karamin hanjinsa.
Tuni shi ma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwolu, ya ziyarci yaron a gadonsa na asibiti inda hotuna suka nuna yaron ya zama tamkar kwarangal, alamun yana jin jiki, nan take dai gwamnan ya ce ya dauki nauyin jinyar da ake wa yaron a asibitin tare da alkawarin daukan matakan da suka dace na gano abin da ya faru ta bangaren asibitin wanda mallakar jihar Legas ne.
Kodayake, kokarin jin ta bakin jami’an lafiya a asibitin ya ci tura, wani ma’aikacin asibitin da ba ya so a ambaci sunansa ko daukan muryarsa, ya sheda wa Muryar Amurka cewa, tun da farko iyayen yaron sun kai shi wani asibiti ne mai zaman kansa inda aka gudanar masa da aikin cire appendix. Sai da lamarin ya yi kamari ne suka garzayo asibitin na gwamnati domin neman sauki.
Sau da yawa dai ansha zargin jami’an lafiya da sakaci wajen kulawa da marasa lafiya, wanda a wasu lokuta yakan kai ga rasa rayukan masu jinya, ko samun nakasa.
Mun kwararren likita a fannin binciken lafiya Mohammad Sani, akan irin abin da ke haifar da irin wannan matsala, ya ce shi ne aiki da yake wa likitoci yawa, domin sauda yawa za a taras likita guda daya yana kulawa da marasa lafiya kusan hamsin a rana ko fiye da haka, don haka duk likitan da ke da aiki ko fede mutane da dama dole kansa ya buga domin babu yadda zai iya.
Dalilin haka ne za ka ga a manta da wani abu a cikin mutum ko yanke abin da bai kamata ba.
Ko a kwanan nan ma dai sai da Majalisar da ke sa ido akan aikin likita a Najeriya ta dakatar da wasu likitoci hudu da aka samu da laifin aikata ba dai-dai ba a lokacin aikin su.
Likitocin sun hada da Dr. Ejike Ferdinand Orji, Dr. Richard Chukwujekwu Okoye da Dr. Olalekan Olatise da kuma Dr. Buliaminu Adebayo Adigun.
A watan Janairun bana ne dai wata babbar kotun Legas ta yanke wa Dr. Ejike Ferdinard Orji daurin shekara daya a gidan yari bayan an same shi da laifin saka ran wani matashi mara lafiya cikin hatsari a matsayinsa na shugaban wani asibiti mai zaman kansa da ke unguwar Dolphin a Legas.
Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibrin:
Dandalin Mu Tattauna