Wata shari’ar da ake yi a Texas da ta shafi dan tsohon shugaban Guinea, marigayi Ahmed Sekou Toure ta jawo hankali a kan batun safarar bil adama domin tilasta musu yin aikin bauta.
An yiwa Mohamed Toure mai shekaru 57 da matarsa Denise Cros-Toure itama mai shekaru 57 daurin talala, suna jiran shari’a bisa zargin kawo wata yarinya mai shekaru biyar daga kasar Guinea suna tilasta mata yin ayyuakn gida ba tare da biyanta albashi ba kuma tana kula musu da yara tsawon shekaru 16
Idan kotu ta yanke musu hukunci bautarwa, zasu iya huskantar daurin shekaru 20.
Ma’auratan da kotu ta kwace passport nasu, sun musunta zargin da ake musu, sun ce mahaifin yarinyar ne ya basu ita su reneta tare da yayansu.
Ma’aikatar shari’a, ta fada a cikin wata sanarwa cewa iyalan Toure sun kawo wata yarinya daga wani kauyen kasar Guinea a shekarar 2000 zuwa gidansu dake Southlake a Texas, inda tayi aiki a matsayin yarinyar gida, da kuma mai renon yara da suka kai biyar, kuma tana fara aiki daga karfe 6 da rabi na safe har sai yaran sun yi bacci.
Ta fadawa jami’ai cewa ba a taba biyanta ba, ba’a sa ta a makaranta ba,kuma ba’a taba kaita asibiti ba, sai dai duka kawai take sha da balat ko kuma wayar lantarki tare da cin zarafinta ta hanyoyi da dama idan Cros-Toure bata gamsu da aikinta ba.
Facebook Forum