Shugaban Amurka Donald Trump ya yi yunkurin kyautata dangantakarsa da Afrika a jiya Litini, yayin da ya amshi bakwancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Buhari, shine shugaban wata kasa kudu da hamadar sahara na farko da shugaba Trump yayi taron koli dashi a fadarsa ta White House, shugaban na Amurka ya sha suka kan kalaman batanci da aka ce yayi ga Afrika.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai tare da shugaba Buhari, Trump ya fi maida hankali ne a kan dacewa da kasashen biyu suka yi wurin bukatu da manufofin yaki da ta’addanci da kuma fadada cinikayya.
Buhari ya godewa Trump a kan amincewa da yarjejeniyar sayerwa Najeriya makamai, lamarin da gwamnatin shugaba Obama taki amincewa da shi bisa zargin take hakkin bil adama.
Kugiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi sojojin Najeriya da azabtarwa da yin fiyade da kuma kisa ba tare da shari’a ba, a yakin kusan shekaru goma da suke yi da kungiyar ta’adda ta Boko Haram.
Da aka tambayeshi ko wannan batu ya taso a tattaunawarsu da Trump, shugaba Buhari yaki cewa uffan.
Yace ina taka tsantsan a kan abubuwa da manema labarai ke fada game da wani ba ni ba. Bani da tabbas a kan ko wannan zargin gaskiya ne ko a’a. Don haka abin da ya dace shine nayi shuru inji Buhari.
Trump ya shiga maganar kai tsaye, yace bamu tattuana komai akai ba, saboda shugaban ya san ni kuma ya san inda na fito. Kuma yace akwai wasu kasashe da suke cikin yanayi mara kyau a wurare da dama.
Facebook Forum