Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Horas Da Kananan Hafsoshi 51 Kan Yaki Da Ta’addanci


Wadannan kananan hafsoshi sun samu horaswa a wani bangare na koyon aikin soja a makarantar NDA dake Kaduna.

Rundunar sojojin Najeriya ta horas da kananan hafsoshi guda 51 kan yadda ake yaki da ta’addanci, kafin su kammala sauke karatunsu a babbar makarantar koyon aikin soja ta Najeriya, NDA, dake Kaduna.

Wadannan daliban kananan hafsoshi, su na daga cikin kashi na 61 na kananan hafsoshin da zasu sauke karatunsu a makarantar ta NDA.

A lokacin da yake jawabi ga daliban a makarantar sojojin kasa dake Jaji asabar din nan, Babban kwamandan makarantar NDA, Manjo-janar Mohammed Idris, yace irin kalubalen tsaron da kasar nan ta ke fuskanta a wannan lokaci, na bukatar a bayar da kyakkayawar horaswa ga kananan hafsoshi ta yadda zasu samu nasarar yakar ta’addanci.

Janar Idris yace wannan shi yasa babbar makarantar horas da sojoji ta Najeriya, NDA, ta yanke shawarar horas da kananan hafsoshi kan yadda ake yakar ta’addanci ko tawaye da sari-ka-noke a ciki da wajen kasar nan.

Shi kuma a nasa bangaren, Kwamandan makarantar horas da sojojin kasa ta Najeriya, Manjo-janar Tukur Buratai, yace an ba kananan hafsoshin horaswa sosai ta yadda jikinsu zai iya jure kowace irin wahala, tare da nazarin dabarun yadda ‘yan ta’adda ke kitsawa da kai hare-hare da yadda zasu iya murkushe su.

Wasu daga cikin abubuwan da aka horas da kananan hafsoshin a kansu sun hada har da dabarun kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda, da rakiyar manyan jami’ai, dabarun gudanar da bincike a wuraren da ake tare motoci da ababen hawa, da yadda ake ganowa da kuma warware nakiyoyi da bama-bamai.
XS
SM
MD
LG