Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Mutum Na Farko Dashen Kodar Alade A Amurka


Dashen Kodar Alade A Jikin Mutum
Dashen Kodar Alade A Jikin Mutum

Likitoci a birnin Boston na jihar Massachusetts da ke Amurka sun ce sun yi nasarar aikin dashen kodar alade da aka canzawa kwayoyin halitta a jikin wani mutum majinyaci mai shekaru 62 da ke da ciwon koda a mataki mai muni.

Sanarwar ta ranar Alhamis ta kasance, karo na farko da aka yi dashen kodar alade zuwa wani mutum mai rai, a cewar Babban Asibitin Massachusetts.

Kokarin da aka yi a baya sun hada da dashe na wucin gadi na bangare jikin mutane da suke bada gudummawa da kwakwalwarsu ta mutu kuma ba’a samu nasara ba a dashen zuciya guda biyu daga aladu.

Dashen Kodar Alade A Jikin Mutum
Dashen Kodar Alade A Jikin Mutum

Likitoci sun ce majinyacin, Richard Rick Slayman na Weymouth da ke Massachusetts, yana samun sauki sosai bayan aikin da aka yi a farkon wannan watan, kuma ana sa ran za'a sallame shi daga asibiti nan ba da jimawa ba.

Wannan matakin na ci gaba da aka samu na yin dashe, da ake amfani da sassan jikin dabba a yiwa mutane magani, tare da kokarin da aka yi na baya bayan nan da ke mayar da hankali wajen sauya kwayoyin halitta gabban jikin alade ya zama ya dace da na mutane, bayan shafe gomman shekaru na rashin nasara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG