Taron addu'ar ya biyo bayan umurnin da Jama'atul Nasril Islam ta bayar na yin addu'o'in. Tsohon ministan noma da na tsaro Dr. Shettima Mustapha na kan gaba a addu'ar. Yace tun shekarar 1966 Shata yayi waka inda yace ana son a taba su yara amma ana tsoron mayan mutane a arewa. To yanzu da aka taba yara ina manyan suke? Idan suna nan ina suka shiga? Banda haka ina samarin suke? Ko samarin sun buturte wa manyan ne? Menene yake faruwa? Abun dake faruwa yanzu ba na Adamawa da Borno da Yobe ba ne kawai. Abun dake faruwa kamar gobara ce ta tashi inda wani yace ba zata taba shi ba to yayi hatara. Yace dole a samu amsa. Kada a yi sakaci wutar ka iya lakume kowa da kowa.
Sheikh Bala Lau shugaban Izala ya bayyana ma'anar Alqunut. Yace idan Musulmai suka samu kansu cikin wani hali Manzon Allah (S. A. W) yace su yi addu'a su kaskantar da kansu so roki Allah Ya kawar da bala'in da ya addabesu. Wannan shi ne Alqunut. Yace sabili da haka suka bada umurni a kungiyance daga nan zuwa wata daya su dukufa suna ta yin istigifari suna Alqunut, suna karatun Kur'ani domin nemawa kasar mafita. Yace domin idan babu zaman lafiya ko salla ma ba za'a iya yinta ba.
Sakamakon addu'a da a keyi Sheik Bala yace yanzu an soma ganin canji. Misali, hukumar tsaro ta SSS ta kama wadanda suka kashe Sheikh Albani. Ya yabawa jami'an da yadda suka zakulo wadanda suka kashe babban malamin Sheikh Albani. Ya roka a yiwa wadanda aka kama shari'a bisa ga doka kuma a gano su wanene a bayansu .
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya