Masu kutse kan internet sun fitar da wasu bayanan mutane masu dinbin yawa wanda sukace bayanan ya kai kusan na mutane Miliyan 50 kuma duk yan asalin kasar Turkiyya.
Bayanan dai sun kushi sunaye da lambar katin dan kasa da adireshin mutanen da kuma ranar haihuwarsu dama sunayen iyayensu. Da gangan cikin takardun aka nuna sunan shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan da na Faras Ministansa Ahmet Davutoglu.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, ya samu damar gwada wasu bayanai na mutane 10 ciki kuwa bayanan mutane 8 ya nuna sahihancin bayanin.
Masu kutsen dai sun kafe wani sako dake cewa, “waye zai taba tunanin cewa tsauraron manufofi da mulkin kama karya da karuwar tsattsauran ra’ayin addini a Turkiyya zai kai ga haifar da rashin tsaro a fannin kundin bayanai.”
Sun kuma kara kafe wani sakon da ke cewa “A koyi darasi” akan tsaron shafin internet.
Idan dai har an tabbatar da wannna kutse gaskiya ne, to zai zamanto babban kutse da aka tabayi wanda ya bayyana bayanan mutanen Turkiyya, kuma ka iya jefa su cikin hatsarin barayi.
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin Amurka ta ce masu kutse sun kai hannusu ga bayanan ma’aikatan gwamnatinta har sama da Miliyan 20, sai dai jami’an sun zargi China.