Jerin sunayen mata da sukafi kudi a duniya, Zhou Qunfei, itace mace ta farko da tafi kowace mace kudi a cikin jerin sunayen mata da suka neman ma kansu kudi batare da dogaro da wani ba. ‘Yar shekatu 46, dai ta mallaki kimanin dallar Amurka billiyan $6B, ‘yar asalin kasar China ce, tana da kamfani mai suna Lens Technology. Sai ta biyu Diane Hendricks, mai shekaru 69, ta mallaki kimanin dallar Amurka billiyan $5.6B, tana sana’ar kayan gine-gine, 'yar asalin kasar Amurka ce. Sai ta uku itace Chan Laiwa, mai shekaru 74, ‘yar asalin kasar China, tana da kamfanonin hada kujeru da kayan kawata gida, tana da adadin kimanin dallar Amurka billiyan $5.2B.
Ta hudu kuwa itace Pollyanna Chu, ‘yar asalin kasar Hong Kong, mai shekaru 58, tana sana’ar hada hadan kudi, tana da adadin kimanin dallar Amurka billiyan $4.9B. Haka ta biyar itace Elizabeth Holmes, wadda ta zama mace ta farko da tasamu kudinta da kananan shekaru, tun tana yar shekaru 19, ta bar karatun jami’a. Ta fara kasuwanci inda ta kirkiri wani kamfani da ke duba lafiya mutane, tana da kimanin dallar Amurka billiyan $4.5B. Yanzu haka tana da shekaru 32 a duniya.
Doris Fisher, ta zama mace ta shida da tafi kudi a duniya, tana da shekaru 84, ita keda kamfanin kayan sawa na Gap, tana da kimanin dallar Amurka billiyan $3.2B. Haka itama Jin Sook Chang, itace ta bakwai a jerin mata masu kudi a duniya, mai shekaru 52, 'yar asalin Amurka, tana da kimanin dallar Amurka $3.1B, itama tana sana’ar kayan sawa.