Dr. Suraiya Mansur Mohammed, likitan daddobi ce daga karamar hukumar Danbatta dake jihar kano, Najeriya. Tayi karatun firamaren ta a makarantar Yandutse Nursery and Primary School dake jihar kano. Sannan ta garzaya makarantar ‘yan mata ta St. Louis dake cikin birnin Kano. Daga bisani ta samu digirin ta na farko a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda ta samu sakamako mai kyau ta zama likitan dabbobi.
Abin alfahari anan shine Dr. Suraiya, tana daya daga cikin mata masu hazaka da suka fito daga jihohin Arewa inda tazama kwararriyar likitan dabbobi da kula da lafiyar dabbobin. Daga nan tayi aiki a ma’aikata mai zaman kanta da ake kira Reach Care Foundation-Nigeria inda ta shugabanci fannin da ya shafi lafiyar dabbobi. A halin yanzu tana kokarin kamala digirin ta na biyu a kasar Amurka, a bangaren kula da lafiyar al’umma gaba daya wato Public Health a jihar Texas.