WASHINGTON D.C —
A shirinmu na mata, a yau muna tare da Hafsat Kabir Matashiya mai Sana'ar kunshi, Hafsat ta ce ta fara sana'ar ne tun tana makarantar firamare kuma a kowacce rana takan yi ma mata sama da goma kunshi musamman idan lokacin kakarsu ce.
Matashiyar ta kara da cewa babu wanda ya koya mata wannan sana'a, kuma a cewar ta tana samun alheri kwarai daga wannan san'a domin a wasu lokuta har Amare ake daukar ta taje tayi masu kwalliya.
Hafsat ta kara da cewa tana shi'awar komawa makaranta domin ta karo karatu kuma ta ce tana shi'awar zama 'yar jarida a rayuwar ta. Kodashike akwai kalubale na rayuwa daban daban, amma Hafsat bata yi kasa a gwiwa ba.
Ga cikakkiyar hirar su da wakiliyar dandalin voa Baraka Bashir daga birnin Kano.