An yi jana'izar marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Danfulani Suntai, wanda ya rasu tun ranar 28 ga watan Yuni shekarar 2017 a garinsa na haihuwa Suntai dake karamar hukumar Bali bayan hidimar karramawa a filin wassani na zamani na Jolly Nyame a garin Jalingo.
Cikin hudubar sa Rt. Rev. Peter Bartimeus na darikar LCCN ya yi nasiha kan ribar mutuwa ga adilai yana kalubalantar jama'a bukatar barin gurbi mai kyau bayan karewar wa'adin su a nan duniya.
Wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, ya yi hira da wasu da suka yi aiki da siyasa tare da marigayin lokacin da yake raye, ko wadanne ayyuka ko halayya al'umar jihar Taraba za su dauki lokaci mai tsawo suna tunawa da shi.
Mataimakin gwamnan jihar Taraba Injiniya Haruna Manu, ya ce al'umar jihar za su rika tunawa da marigayin saboda rungumar da ya yi wa kowa da kuma kafa jami'ar jihar Taraba. Yayin da Hon. Victor Bala Kona shugaban jam'iyar PDP ya ce marigayi Danbaba mutun ne mai tsare gaskiya.
A sakonnin ta'aziyya da wasu daga cikin gwamnoni da tsoffin gwamnoni da suka halarci jana'izar akwai gwamna Fayoshe na jihar Ekiti, wanda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kamanta gaskiya da adalci da tsoron Allah.
Gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Ishaku, hakuri ya baiwa iyalan marigayin da suka hada da mai dakinsa Hauwa Danbaba Danfulani Suntai da kuma al'umar karamar hukumar Bali da jihar Taraba.
Marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Danfulani Suntai, dan shekar 56 da haihuwa ya gamu da ajalinsa bayan doguwar jinya sakamakon hatsari da jirgin sama da yake tukawa da kansa a Yola fadar jihar Adamawa ranar ashirin 20 ga watan Oktobar 2015.
Kamin rasuwarsa Marigayi Danbaba Danfulani Suntai ya yi mulkin jihar Taraba na tsawon shekaru shida, ya rasu ya bar matarsa Hauwa Danbaba Danfulani Suntai da 'ya'ya biyar da Jika ‘daya.
Domin karin bayani ga rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum