Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Fafaroma Benedict Na 16 A Vatican


Jana’izar Pope Benedict Na 16
Jana’izar Pope Benedict Na 16

Yau aka yi jana’izar Fafaroma Emeritus Benedict na 16, wanda ya rasu yana da shekaru 95 a ranar 31 ga watan Disamba, a birnin Vatican, bayan nan magajinsa Fafaroma Francis zai shugabanci wata hidima da za a gudanar.

WASHINGTON, D. C. - Benedict ya kafa tarihi a shekara ta 2013 inda ya zama Fafaroma na farko a cikin shekaru 600 da ya sauka daga mulki, kuma ya yi suna wajen dawo da kyakykyawan ra'ayin mazan jiya ga Cocin Roman Katolika, amma Fafaroma Francis ya fito da wata hanya daban tun bayan da ya karbi mulki.

Kimanin mutane 50,000 ne suka halarci jana’izarsa, a cewar fadar Vatican, bayan da wasu 200,000 ne suka nuna girmamawa da bankwana da shi a cikin kwanaki uku.

-AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG