Fadar Vatican ta fadi jiya Asabar cewa Archbishop Pietro Parolin, wanda wani tsohon Mataimakin Ministan Harkokin Waje ne a Vatican, zai dau mukamin Sakataren Harkokin Waje ran 15 ga watan Oktoba.
Parolin dan shekaru 58 da haihuwa, a yanzu haka shi ne Jakadan Vatican a Venezuela.
Wannan nadin ya kawo karshen zamanin Cardinal Tarcisio, wanda akasari ke dora wa laifin kasa kawar da tabargazar ka’ida da kuma kudi, wadda ta bullo yayin shekaru 8 da tsohon Paparoma, Pope Benedict ke Paparoma.
Nadin sabon Sakataren Harkokin Wajen shi ne nadi mafi girma da Paparoma Francis ya yi, tun bayan zabensa da aka yi a cikin watan Maris. Sakataren Harkokin Waje ne ke rika ma Paparoma a duk lokacin da bai da lafiya, kuma shi ke gudanar da sha’anin hukumar ta Vatican da ake kira Curia. Ya na taka rawa a sha’anin kudi da nada bishop-bishop da kuma harkokin diflomasiyya da kasashe sama da 170.