Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Lakcarar Jami'ar Maiduguri Da Aka Yi Wa Kisan Gilla


Dr Kamal Abdulkadir
Dr Kamal Abdulkadir

An gudanar da jana'izan Dr Kamal Abdulkadir na jami'ar Maiduguri, malami a bangaren ilimin jiki da lafiya da aka yi wa kisan gilla.

Hukumomin Jami’ar Maiduguri sun tabbatar da kashe Dokta Kamal Abdulkadir, a ofishinsa ranan Lahadi.

Dokta Kamar yakan zo aiki a duk ranakun hutun mako inda hakan ya kai ga wasu da ba a san ko su wanene ba suka kashe shi a ofishinsa tare da sassare sassan jikinsa da gatari da ma daba masa wuka a ciki.

Maharan dai sun tafi da motar sa dama wayansa amma sun bar hadda da wuka a ofishinsa.

Jana'izar Dr Kamal Abdulkadir
Jana'izar Dr Kamal Abdulkadir

Gawar Dr Kamal Abdulkadir ta kwana a ofishinsa inda iyalansa suka zo ofishinsa da safiyan Litinin suka iske gawarsa tare da sassan jikinsa da aka sassare.

A wata sanarwa da aka fitar ta bakin Farfesa Danjuma Gambo, kakakin jami’ar ya tabbatar da faruwan lamarin.

Sanarwan ta bayyana yadda aka tsinci gawarsa a ofishinsa da safiyan Litinin.

Daya daga cikin abokansa malamai Ali Galadima, ya ce lamarin ya tayar musu da hankali sosai.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Borno, ASP Naso Nahun Kenneth ya tabbatar da faruwan lamarin ya ce yanzu haka suna tsare da wasu mutane takwas da ake zargi da aikata kisan tare da dauke masa mota, yanzu haka suna bincike akai.

Saurari rahoton Ibrahim Mustapha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG