Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Babban Wasan Kwallon Kafa Na Farko Cikin Shekaru 30 a Mogadishu


'Yan wasan kungiyar Hodan (Jajaye) suna taka leda da abokanan hamayyarsu na Waberi (dorawa) a wasan kwallon kafa da aka yi na farko cikin shekaru 30 a Mogadishu
'Yan wasan kungiyar Hodan (Jajaye) suna taka leda da abokanan hamayyarsu na Waberi (dorawa) a wasan kwallon kafa da aka yi na farko cikin shekaru 30 a Mogadishu

An yi babban wasan kwallon kafa na farko cikin shekaru 30 a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, wasan da ya samu halartar dubban masu kallo ya kuma zama tarihi.

A karon farko cikin shekaru 30, dubban jama’a sun taru a filin wasan kwallo na birnin Mogadishu domin kallon wani wasan dare da aka yi a birnin, wanda ake kwatantawa a matsayin wanda yafi kowane hadari a duk fadin duniya.

Dubban masoya kwallon kafa ne suka taru a filin wasan Konis, wanda hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta gyara.

Koda yake wasan na karshe ne a wata gasar matasa masu shekaru 16 zuwa 18 da aka hada, amma ya kasance cikin tsauraran matakan tsaro, kuma abin tarihi ga birnin na Mogadishu, wanda ya ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Bayan wasan wanda kungiyar Waberi ta doke Hodon da ci 3-0, Magajin Garin Mogadishu, Tabit Abdi Mohamed ya ce, al’umar birnin sun cancanci su sami cikakken tsaro a koda yaushe, ba wai kawai sai za a yi wasan kwallo ba.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG