Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-shabab Ta Kasar Somalia Ta Kai Hari


Hari bom din da aka kai da mota a Jos, Mayu 22, 2014.
Hari bom din da aka kai da mota a Jos, Mayu 22, 2014.

Kungiyar Al-Shabab ta kai harin kunar bakin wake kuma har mutane 7 sun mutu

Kungiyar Al-Shabab ta kasar Somalia ta kai wani harin kunar bakin wake da mota a wani barikin sojin Somaliya, inda ta hallaka sojoji akalla 7 a wurin, wanda ke arewa da birnin Kismayo, kamar yadda jami'an lardin mai hedikwata a Kismayo su ka gaya ma Muryar Amurka.

Jami'an su ka ce mayakan sun tayar da bama-baman da ke makare cikin motoci biyu a wani wurin da sojoji ke duba ababen hawa kafin wasu mayaka dauke da muggan makamai su ka abka ma sansanin sojin, wanda ke garin Bulogudud, da safiyar jiya Lahadi.

Wani mai magana da yawun hukumar lardin Jubbland, mai suna Abdinasir Serar, ya gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa sojoji sama da 10 ne su ka samu raunuka a wannan harin, wanda aka kai da asuba.

Su dai mayakan al-Shabab, sun yi ikirarin hallaka sojojin gwamnati har guda 26, banda motoci da kuma makaman da su ka ce sun kwato.

Sai dai babu wata majiyamai zaman kanta da ta tabbatar da ko daya daga cikin rahotannin biyu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG