Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenyatta Na Duba Yiwuwar Sauya Fasalin Fannin Shari'a


Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, bayan da kotu ta soke nasarar da ya samu a zaben da aka yi a watan jiya, ranar 2 ga watan Satumba 2017. (Facebook/@myuhurukenyatta)
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, bayan da kotu ta soke nasarar da ya samu a zaben da aka yi a watan jiya, ranar 2 ga watan Satumba 2017. (Facebook/@myuhurukenyatta)

Gwamnatin Uhuru Kenyatta na duba yiwuwar sake fasalin fannin shari'ar kasar, bayan da kotun koli ta soke zaben da ya bashi nasara a watan da ya gabata.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce akwai bukatar a yi wa fannin shari’ar kasar gyaran fuska, bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben da ya bashi nasara a watan da ya gabata, inda aka yi zargin tafka kurakurai.

A karo na biyu kenan cikin kwanaki biyu, shugaba Kenyatta yake caccakar kotun, inda ya zarge ta da yin watsi da ra’ayin jama’ar kasar bayan da ta soke zaben.

Kenyatta ya yi ta kalamai marasa dadi akan kotun, inda ya ke tambayar shin waye ya zabi alkalan kotun, yana mai cewa, lallai akwai kurakurai a fannin shari’ar kasar, kuma lokaci ya yi da za a yi gyara.

Shugaban na Kenya ya yi wadannan kalaman ne ta kafar talbijin a Fadarsa da ke Nairobi babban birnin kasar.

Ita dai kotun kolin kasar ta soke zaben ne bayan da ta tabbatar cewa an samu kurakurai ta gefen hukumar zabe.

Sai dai duk da korafin da yake yi, a ranar juma’ar da ta gabata, shugaba Kenyatta ya ce zai bi umurnin kotun, duk da cewa a gashin kansa bai amince da matsayar kotun ba.

Shugaban ‘yan adawa Raila Odinga ne, ya shigar da karar neman a soke zaben, yana mai cewa yawan kuri’un da Kenyatta ya samu da suka kai miliyan1.4, duk na bogi ne.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG