Kungiyar rajin Amnesty International ta ce kusan fararen hula 400 aka kashe a kasashen Kamaru da Najeriya sanadiyar hare-haren kunar bakin wake da ‘yan kungiya Boko haram suka kai tun daga watan Afirilun wannan shekarar, wanda ya fi linkin hare-haren da ‘yan kungiyar suka kai cikin watanni 5 kafin watan Afrilu.
Wani rahoto da kungiyar ta kare hakkokin bil’adama ta fidda yau Talata ya ce, akalla fararen hula 223 mayakan boko haram suka kashe tun daga watan Afrilu, ciki harda fararen hula 100 da aka kashe a watan Agusta kadai. An kuma kai wani mummunan hari ranar 25 ga watan Yulin wannan shekarar, lokacin da aka harbe mutane 40 har lahira a wani kwanton bauna da mayakan boko haram suka yiwa wata tawagar masu hakar man fetur a jihar Borno. Kungiyar Amnesty ta ce ta yiwu adadin wadanda suka rasa rayukansu ya fi haka, saboda ta yiwu ba a sami rahoton wasu hare-haren da aka kai ba.
A makwabciyar Najeriya kuma, Kamaru, an kashe akalla fararen hula 158 sanadiyar hare-haren kunar bakin wake tun daga watan Afrilu, ciki harda harin bom din da aka kai a wani wurin wasa a birnin Waza, ranar 12 ga watan Yuli wanda ya hallaka mutane 16. Kungiyar ta Amnesty International ta ce ta yiwu fatattakar ‘yan boko haram da dakarun Najeriya suka yi daga dajin Sambisa, zuwa tsaunukan Mandera shi ya kawo karuwar hare-haren a kasar Kamaru.
Facebook Forum