An shiga takun saka tsakanin Shiyyar Arewa Maso Gabas da Shiyyar Arewa Maso Tsakiya kan mukaman Majalisar Tarayya, musamman ma mukaman Shugaban Majalisar Dattawa da na Kakakin Majalisar Wakilai da sauran manyan mukamai.
Wakilnmu a Abuja Hassan Maina Kaina, ya ruwaito wani tsohon dan Majalisar Wakilai daga Arewa Maso Gabas mai sauna Dokta Almajiri Gaidam, wanda ke jagorantar wani gungun ‘yan siyasar yankin masu son yankin ya samu mukaman, na cewa, “ Sashin mu na Arewa Maso Gabas na neman manyan mukamai biyu a kowacce daga cikin majalisun – a Majalisar Dattawa su samu matsayi guda a Majalisar Wakilai ma mu samu guda. Idan zai yiwu ma a ba nu Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, ko kuma a ba mu Kakakin Majalisar Wakilai da kuma Mataimakin Shuagaban Majalisar Dattawa. Hujja ta kuwa it ace, mu na da kujeru da yawa – a Majalisar Dattawa mu na da kujeru 13, a Majalisar Wakilai kuma mu na da kujeru 41.”
To saidai a nasu bangare kuma na Arewa Maso Tsakiya, Kakakin jam’iyyar APC a jihar Naija, Mista Jonathan Batsa ya ce su ne su ka fi cancantar a ba su wadannan mukaman. Ya ce, “Domin mu na da kwararrun ‘yan siyasa da mu ka san za su iya rika wadannan mukaman kuma mun san wasu mutanenmu na so. Amma mun san cewa manyanmu za su zauna a daidata a yi magana.” Da wakilnmu n ace masa wasu za su ga kamar bai kamata su nemi wannan matsayi ba ganin cewa Shugaban Majalisar Dattawa na yanzu , Sanata David Mark dan yankin ne, sai ya ce, ai batun siyasa wani sa’in ba yadda wasu ke gani yak an kasance ba. Yace kodayake David Mark ya yi shekaru 8 a mukamain, a jam’iyyar PDP ne ya yi, ba a APC ba. To saidai wani jigon jam’iyyar ta APC mai suna Sabo Imamu Gashua, y ace muddun jam’iyyar APC ba ta hada kai kan wannan al’amara na mukami ba, to ta na iya samun Baraka.